Wasanni

Morocco ta dauki sabon mai horaswa

Sabon mai horas da tawagar kwallon kafar Morocco, Vahid Halilhodzic.
Sabon mai horas da tawagar kwallon kafar Morocco, Vahid Halilhodzic. REUTERS/Stephane Mahe

Morocco ta bayyana Vahid Halilhodzic a matsayin sabon mai horas da tawagar kwallon kafar ta.

Talla

Sabon kocin na Morocco mai shekaru 67 ya taba horas da tawagogin kwallon kafa na kasashen Ivory Coast da Algeria, kasar da shekarar 2014 ya kai ta matakin zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya, nasarar da ta zama irinta ta farko da kasar ta Algeria ta samu.

Halilhodzic wanda tsohon kocin kasar Japan ne, ya karbi ragamar horas da Morocco bayan ajiye aikin da Harve Renard yayi, saboda tabuka abin azo a gani a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta bana, inda a halin yanzu ya karbi aikin horas da ‘yan was an Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.