Isa ga babban shafi
DR Congo-Ebola

An sake samun bullar Ebola a Congo

Jami'en kiwon laiya yayin allurar rigakafin cutar a garin Goma na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
Jami'en kiwon laiya yayin allurar rigakafin cutar a garin Goma na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo REUTERS/Djaffer Sabiti
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 2

Mahukunta a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, sun ce mutane biyu sun kamu cutar Ebola a yankin Kudancin Kivu, wanda shi ne karo na farko da aka samu wadanda ke dauke da kwayoyin wannan cuta, yayin da tuni daya ya mutu.

Talla

Mataimakin sakataren yada labarai a fadar shugaban kasar ta Congo Giscard Koussema, wanda kuma mamba ne a kwamitin yaki da wannan annoba a kasar, ya tabbatar da wannan al’amari, inda ya ce wata mata da kuma danta da suka fito daga garin Beni ne a arewacin Kivu suka kamu da cutar.

Ya ce a halin da ake ciki,jami’an kiwon lafiya sun killace wannan yanki, sannan ana ci gaba da aikin tantance wadanda suka yi cudanya da wadannan mutane biyu.

Yanzu haka daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar wanda ke raye, na karkashin kulawar jami’an kiwon lafiya.

To sai dai birin Bukavu mai tazarar kilomita 500 daga inda aka samu bullar annobar yana fuskantar barazana, amma dai ana ci gaba da sa-ido sosai dangane da jama’ar da ke shiga yankin na Kudancin Kivu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.