Tubabben sarkin Abéché na kasar Chadi yaki fitcewa daga fada
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yanzu haka jami'an tsaro a kasar Chadi na kokwarin kwantar da hankula a wata masarautar Abeche dake Gabashin kasar a kokarin su na fitar da sarkin garin da iyalansa da mahukunta suka tube tare da maye gurbin sa da wani.Watanni da dama kenan bayan tsige shi daga karagar mulki, Sarkin kabilar Ouaddai da ke da babbar fadarsa a garin Abeche da ke Gabashin kasar Chadi ya ki fita daga wannan fada.Kuma duk da yunkurin yin amfani da jam'an tsaro da mahukunta suka yi domin fitar da shi, amma hakan ya gagara, sakamakon yadda dangi da kuma kabilar sarkin ke ci gaba da nuna tirjiya.watanni da sukagabata mahukuntan kasar suka sauke sarkin tare da maye gurbin sa da wani, sakamakon yawaitar tashin hankali da ake samu tsakanin kabilun makiyaya da Manomar yankin da ake ganin tsohon sarkin na da hannu a ciki, wajen baiwa kabilar sa ta Ouaddai fifiko.Dangane da wannan batu Sarkin Hausawan Ndjamena Alhaji Mustapha Ibrahim, ya yi mana karin bayani.
Latsa don sauraron karin bayani daga bakin sarkin hausawan Ndjamena Alhaji Mustapha Ibrahim.
Alhaji Mustapah Ibrahim, sarkin hausawan birnin Ndjamena, kan rikicin masarautar Ouaddai na Abeche a Gabashin kasar Chadi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu