Isa ga babban shafi
Gabon

Ali Bongo ya bayyana ga jama'a karon farko cikin watanni 10

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo, yayin halartar bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar daga Faransa.
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo, yayin halartar bikin zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar daga Faransa. Steve JORDAN / AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Shugaban Gabon Ali Bongo, ya halarci bikin zagayowar ranar yancin kasar, karo na farko da shugaban ke bayyana ga bainar jama’a, tun bayan rashin lafiyar mutuwar barin jikin da ya fara watanni 10 da suka gabata.

Talla

A watan Oktoban shekarar bara shugaba Ali Bongo ya soma fama da mutuwar barin jiki, yayin wani taron tattalin arzikin da yake halarta a Saudiya.

A jiya Juma’a ne dai Gabon tayi bikin zagayowar ranar samun yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

Cikin watan Janairu na wannan shekara, shugaban kasar ta Gabon, Ali Bongo Ondimba ya koma gida bayan kwashe watanni yana jinya a kasashen waje sakamakon bugun zuciyar da ya samu lokacin da yake halartar taro a Saudi Arabia.

Cikin watan na Janairu ne kuma hukumomin tsaron kasar ta Gabon suka tabbatar da kashe biyu daga cikin sojojin da suka jagoranci yunkurin juyin mulkin kasar a yau Litinin baya ga kame jagoransu dai dai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da tir da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.