Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Condo

Cutar Kyanda ta fi Ebola barna a Jamhuriyar Congo - MSF

Wani dan Jamhuriyar Congo, yayin karbar allurar rigakafin kamuwa da cutar Ebola a birnin Goma.
Wani dan Jamhuriyar Congo, yayin karbar allurar rigakafin kamuwa da cutar Ebola a birnin Goma. Reuters/Baz Ratner
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF, ta ce adadin hasarar rayunkan da cutar Kyanda ta haddasa a jamhuriyar Congo cikin shekara guda ya zarta barnar da annobar cutar Ebola ta yi na halaka mutane kusan dubu 2.

Talla

Likitocin sun ce cikin shekara daya, cutar Kyanda ta halaka mutane akalla dubu 2 da 758 a Jamhuriyar ta Congo, kuma yanzu haka 'yan kasar dubu 145 ne suka kamu da cutar, daga watan Janairun wannan shekara zuwa farkon Agusta.

Kan haka ne kuma kungiyar likitocin ta bukaci gaggauta cika alkawurin da manyan kasashe dasauran kungiyoyi suka dauka na samar dadala miliyan 8 da dubu 900, don yakar cutar ta Kyanda, wanda zuwa yanzu dala miliyan 2 da rabi kawai aka samu.

Cikin watan Agusta, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce adadin wadanda ke kamuwa da cutar kyanda ko bakon-dauro a duniya ya ninka sau uku cikin watannin bakwan farko na wannan shekara, idan aka kwatanta da shekarar bara ta 2018.

Hukumar ta WHO, da ta danganta fuskantar matsalar da yadda mutane ke bijirewa bukatar yi wa ‘ya’yansu rigakafi, ta ce zuwa yanzu cikin watanni bakwan farko na wannan shekarar, yara dubu 364, da 808 ne suka kamu da cutar Kyandar, sabanin 129, da 239 da suka kamu da cutar a bara.

Rahoton hukumar lafiyar ya kara da cewa, kasashen Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, Madagascar, da kuma Ukraine ne ke kan gaba wajen fuskantar karuwar bullar cutar ta Kyanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.