Najeriya ta lashe kofin gasar kwallon kwandon mata
Wallafawa ranar:
Tawagar kwallon kwandon Najeriya D’ Tigress ta sake lashe kofin gasar kwallon kwandon Nahiyar Afrika ta mata.
Karo na biyu a jere kenan da Najeriya ke lashe gasar kwallon kwandon yayinda a jimlace ta lashe kofin sau hudu, a shekarun 2003, 2005 da kuma 2017 sai kuma na bana.
A ranar Lahadi ‘yan matan na Najeriya suka lallasa takwarorinsu na Senegal mai masaukin baki, da kwallaye 65 da kuma 55.
A shekarar 2017 ma dai an fafata wasan karshen gasar ce tsakanin kasashen biyu, inda Najeriyar ta doke Senegal da kwallaye 65 da kuma 48.
A wasannin baya da ta fafata yayin gasar, Najeriya ta lallasa Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo da kwallaye 79 da 46.
Tunisia kuwa ta sha kashi a hannun D’ Tigress ne da kwallaye 76 da 25, sai kuma Kamaru da Najeriyar ta yiwa Dukan kawo wuka da kwallaye 106 da 39.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu