Kamaru

An yi wa jagoran 'yan awaren Kamaru daurin rai da rai

Jagoran 'yan awaren Kamaru Julius Sisiku Ayuk Tabe
Jagoran 'yan awaren Kamaru Julius Sisiku Ayuk Tabe YouTube

Kotun Sojin Kamaru ta yanke wa jagoran ‘yan awaren kasar da wasu mukarrabansa hukuncin daurin rai da rai bayan ta same da laifin ta’addanci da kuma raba kan al’ummar kasar.

Talla

Lauyan Gwamnatin Kamaru, Martin Luther ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, an yanke wa Julius Sisiku Ayuk Tabe da wasu mabiyansa 9 hukuncin daurin rai da rai, yayinda lauyan ‘yan awaren, Joseph Fru ya caccaki wannan hukuncin.

Kodayake kawo yanzu, lauyan ‘yan awaren bai sanar da aniyarsu ta daukaka kara ba don kalubalantar hukuncin kotun sojin.

Mr. Ayuk Tabe, mai shekaru 54 kuma masanin fasahar Kwamfuta, shi ne mutun na farko da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar Ambazonia wadda ta balle , sannan ta sanar da kafuwarta a cikin watan Oktoban 2017 a yankunan masu magana da Turancin Ingilishi a Kamaru.

Gwamnatin Kamaru ta mayar da martani ta hanyar amfani da sojoji don murkushe yunkurin kafa kasar ta Ambazonia.

Artabun da aka yi tsakanin bangarorin biyu, ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 1 da 850 kamar yadda Kungiyar da ke Sa ido kan Rikice-Rikice ta Kasa da Kasa ICG ta sanar, yayinda Majalisar Dinkin Duniya ta ce, mutane 530 sun kaurace wa muhallansu saboda tashin hankalin.

A watan Janairun shekarar 2018 ne, aka cafke Ayuk Tabe da wasu mutane 46 a birnin Abuja na Najeriya, inda aka mika su ga hukumomin Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI