Isa ga babban shafi

Adadin Sojin Burkina Faso da harin ta'addanci ya hallaka sun kai 24

Wasu sojojin Burkina Faso
Wasu sojojin Burkina Faso AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Rundunar Sojin Burkina Faso ta sanar da cewa adadin sojojin kasar da suka rasa rayukansu yayin harin ta'addanci da wasu 'yan bindiga suka kai musu ranar Litinin din makon nan ya karu zuwa Sojoji 24. 

Talla

Harin na ranar Litinin wanda ake dora alhakinsa kan mayakan da ke ikirarin jihadi a yankin Sahel, ya faru ne a yankin Koutoubou da ke arewacin gunduman Soum na kasar Burkina Faso, lokacin da mayakan suka musu kwanton bauna.

A cewar rundunar sojin kasar ta Burkina Faso, baya ga sojojin 24 da suka rasa rayukansu akwai kuma wasu soji 7 da yanzu haka ke jinya yayinda wasu karin biyar kuma suka batan dabo bayan farmakin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.