Uganda ta toshe hanyar sadarwar wata jaridar Rwanda a kasar ta

Shugabannin kasashen Uganda Museveni da na Rwanda Paul Kagame
Shugabannin kasashen Uganda Museveni da na Rwanda Paul Kagame Michele Sibiloni / AFP

A yau Juma’a, Kasar Uganda ta bayyana cewa ta toshe kafar sadawa ta babbar jaridar kasar Ruwanda dake tsokaci kan harkokin tsaron kasa a yanar gizo.kwanaki biyu kenan bayan da kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen takun saka da ya yi sanadiyar rufewar iyaka da ta hadasu har na tsawon wattani shida.

Talla

A cewar shugaban Hukumar da ke lura da kafafen sadarwa ta kasar Uganda Godfrey Mutabazi, an bukaci dukkan kafafen internet a kasar da su toshe hanyar da ta hada kasar da kafar jarida New Times, wacce ke da mabiya da dama, a kasar da ke magana da harshen turancin ingilishi dauke da al’ummar kasar Ruwanda da dama.

Ya zuwa wannan lokaci dai ba’a samu martani ba daga gwamnatin kasar Rwanda game da wannan hukunci da hukukar kasar Uganda ta dauka.

A ranar Laraba ne shugabanin kasashen biyu su ka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a babbar birnin Angola, inda su ka amince da mutunta juna da kuma kauracewa dukkan abin da zai janyo tashin hankali a tsakaninsu tare da gaggauta maido da ayyuka a iyakokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI