Jamhuriyar Demokradiyyar Condo

Sabon rikici ya barke a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo

Wasu jami'an tsaro a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo
Wasu jami'an tsaro a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Radio Okapi/Ph. John Bompengo.

Rahotanni daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun bayyana cewa wani sabon fada ya barke a yankin arewa maso gabashin Ituri tsakanin wasu ‘yan bidiga masu bijerewa gwamnati da jami’an tsaro.

Talla

Wata majiyar Sojin kasar ta bayyana cewa rikicin yayi sanadin mutuwar sojin kasar 3 yayinda sojin suka yi nasarar hallaka ‘yan bindiga 20.

Ko cikin watan Yunin da ya gabata ma, makamancin rikicin sai da ya hallaka fararen hula 160 baya ga ‘yan bindigar da kuma jami’an tsaron gwamnati.

A ranar 2 ga watan Yulin da ya gabata ne, shugaba Felix Tshisekedi ya yi umarnin fara wani atisayen soji a yankin don kakkabe ‘yan bindigar da ke barazana ga yankunan Djugu da Mahagi mai arzikin ma’adinai.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kawo yanzu mutane dubu dari 3 ne suka tsere daga yankin sanadiyyar ta’azzarar rikicin wanda kan kai ga kisan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.