Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana dambarwa kan motocin yakin da aka shigo da su Najeriya

Kawo yanzu mahukuntan kasashen Najeriya da Kamaru da Nijar ba su fayyace ainihin mamallakin motocin yakin masu silke da aka shigo da su Najeriya ba.
Kawo yanzu mahukuntan kasashen Najeriya da Kamaru da Nijar ba su fayyace ainihin mamallakin motocin yakin masu silke da aka shigo da su Najeriya ba. Daily Trsut
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Ana ci gaba da samun dambarwa dangane da hakikanin mamallakin motocin yaki masu silke guda shida da jami ‘an tsaron Najeriya suka kama a kan iyakar kasar da Kamaru da ke garin Konkol na karamar Hukummar Maiha ta jihar Adamawa.

Talla

Majiyoyi sun ce, an yi nufin isar da motocin yakin ne ga hukumomin Jamhuriyar Nijar, amma kawo yanzu mahukuntan kasashen Najeriya da Kamaru ba su fayyace ainihin mamallakin motocin ba.

A yayinda bayanai ke cewa, gwamnatin Nijar ce mamallakiyar motocin yakin, wasu rahotanni cewa suka yi, na Kamaru ne, yayinda wasu majiyoyin suka danganta motocin da kasar Amurka.

Tuni Kwamandan bataliyar sojoji ta 23, S.G. Mohammed ya mika motocin yakin ga Hukumar Hana Fasa Kauri wato Kwastam, reshen jihar Adamawa da Taraba.

Hukumar Kwastam ta shirya gudanar da taron manema labarai kan wannan dambarwa a birin Yola, amma daga bisani aka soke taron saboda an mika batun ga hukumomin birnin tarayya Abuja.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, a halin yanzu, shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kanar Hameed Ali mai ritaya, ya bayar da umarnin gudanar da bicnike kan al’amarin.

Majiyar Kwastam ta ce, an kama motocin ne saboda rashin takardun izinin safarar su zuwa wata kasa, yayinda wasu bayanan ke cewa, gwamnatin Amurka ce ta yi wa sojojin kasar Nijar kyautar motocin.

A cewar wasu rahotanni, hukumomin Amurka sun yi mamaki game da kame motocin, inda suka dora laifin aukuwar haka kan rashin musayar bayanai tsakanin jami’an tsaron Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.