Tanzania-Burundi

Tanzania za ta mayar da 'yan gudun hijira dubu 200 Burundi

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Burundi da ke samun mafaka a sansanin Tanzania
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Burundi da ke samun mafaka a sansanin Tanzania REUTERS/Thomas

Gwamnatin Tanzania ta sanar da shirinta na mayar da ‘yan gudun hijirar Burundi kimanin dubu 200 kasarsu, inda ta ce, Majalisar Dinkin Duniya za ta sanya ido kan shirin.

Talla

Gwamnatin Tanzania ta ce, daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa ne za ta fara mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa Burundi, inda a kowanne mako za a rika kwashe mutane akalla dubu 2 har su kare.

Sai dai Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta hakikance cewa, ya kamata a bai wa kowanne dan gudun hijirar damar komawa Burundi domin ratsin kansa.

‘Yan gudun hijirar sun kaurace wa Burundi ne sakamakon kazamin rikicin siyasar da ya barke a shekarar 2015 bayan shugaba Pierre Nkuruziza ya sanar da aniyarsa ta sake komawa kan karagar mulki a wa’adi na uku.

Kodayake an sake zaben sa a cikin watan Yulin shekarar ta 2015, amma duk da haka kasar ta tsunduma cikin tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 1 da 200, yayinda sama da mutane dubu 400 suka kaurace wa gidajensu kamar yadda Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC ta sanar.

A halin yanzu dai, gwamnatin Tanzania ta shaida wa ‘yan gudun hijirar cewa, su koma gidajensu saboda an samu zaman lafiya a Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI