Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi: Mutane 11 sun mutu a sabon rikicin manoma da makiyaya

Wasu manoma zaune a karkashin bishiya, a gafen hanyar da ta hada yankunan Adre da Farchana, a gabashin kasar Chadi.
Wasu manoma zaune a karkashin bishiya, a gafen hanyar da ta hada yankunan Adre da Farchana, a gabashin kasar Chadi. AFP/Amaury HAUCHARD
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Gwamnatin Chadi ta ce mutane 11 sun rasa rayukansu a wani rikici da ya barke, tsakanin manoma da makiyaya a kudancin kasar.

Talla

Rikicin ya samo asali ne daga takaddama kan wata gona da dabbobi suka lalata.

Rikicin ya soma ne tun a ranar litinin da ta gabata, a yankin Koumogo dake lardin Moyen-Chari kamar yadda gwamnan lardin Abbadi Sahir ya tabbatar.

Wani mai sarautar gargajiya dake yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce da fari wasu da ba’a san ko su waye ba ne suka halaka wani makiyayi, bayanda da dabbobinsa suka yiwa wata gona kutse, hakan tasa ‘yan uwansa shan alwashin daukar fansa, inda suka afkawa wata unguwar manoma da muggan makamai, inda lamari ya rincabe.

Sai dai yanzu haka an girke jami’an tsaro don tabbatar da doka da oda, yayinda gwamnatin lardin na Moyen-Chari ke jagorantar sasanta bangarorin biyu.

An dai jima ana samun rikici tsakanin manoma da larabawa makiyaya a Chadi, mafi akasari kuma takaddama kan mallakar filaye ke haddasa tashin hankalin.

A wannan wata na Agusta shugaban Chadi Idris Deby ya yi shelar kafa dokar ta baci lardunan Sila da Ouaddai, bayan mutuwar mutane 50 a rikicin kabilancin da ya barke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.