Isa ga babban shafi
Najeriya

Kusan 'yan Najeriya dubu 2 sun mutu a hare-haren 'yan bindiga- Gwamnati

Wasu 'yan bindiga a Birnin Gwari na jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Wasu 'yan bindiga a Birnin Gwari na jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya. Solacebase
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, mutane dubu 1 da dari 4 da 60 sun rasa rayukansu a hare-hare har guda 330 da ‘yan bindiga suka kaddamar a cikin watanni bakwai da suka gabata, musamman a yankunan Arewa maso yammacin kasar .

Talla

A cewar Dr Amina Shamaki jami’ar da ke kula da ayyuka na musamman a Ofishin babban sakataren gwamnatin Najeriyar yayin wani taro kan al’amuran tsaro da ya gudana a jihar Kebbi, ta ce adadin na daga cikin alkaluman da bincikensu ya nuna.

Dr Shamaki ta bayyana cewa kawo yanzu kalubalen tsaro shi ne babban abu dubawa musamman a yankunan arewa maso yammacin kasar da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Babbar jami’ar gwamnatin Najeriyar ta bayyana cewa hare-haren sun faru ne daga watan Janairun bana zuwa Yuli, ko da dai ta ce an samu raguwar hare-haren ‘yan bindiga cikin watan Yuni da Yulin musamman a jihar Zamfara.

Sai dai a zantawar sashen hausa na RFI da Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, Sarkin Shaun Shinkafi, ya kalubalanci adadin na Gwamnatin Najeriya yana mai cewa ko iya adadin mutanen da aka kashe a jihar Zamfara kadai sun zarce alkaluman gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.