Isa ga babban shafi
Sudan

Daga Saudiya na samu makudan kudaden dake gidana - Al Bashir

Tsohon shugaban Sudan Omar Al Bashir.
Tsohon shugaban Sudan Omar Al Bashir. Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Tsohon shugaban Sudan, Oumar Al - Bashir ya sake gurfana gaban kotu, inda yake fuskantar tuhuma kan aikata laifukan cin hanci da rashawa, da mallakar kudaden kasashen ketare ta haramtaciyyar hanya, da kuma yin amfani su ba bisa ka’ida ba.

Talla

Alkalin dake sauraron shari’ar ta Al-Bashir, Al-Sadiq Abdul RHman, ya ce jami;an tsaro sun samu kashin kudaden ketare har uku a gidan tsohon shugaban na Sudan, da suka hada da fam miliyan 6 da dubu 900, dala dubu 351 da 770 da kuma fam din kasar ta Sudan miliyan 5 da dubu 700.

Yayin da yake amsa tuhumar, Oumar al-Bashir ya ce sukkanin kudaden ya same su ne daga wasu ‘ya’yan gidan sarautar Saudiyya.

A halin da ake ciki, kotun ta Sudan ta dage ci gaba da zaman shari’ar har zuwa ranar 7 ga watan Satumba mai kamawa.

A watan Afrilu dubban ‘yan kasar dake zanga-zangar kin jinin gwamnati suka tilasatawa Oumar Al-Bashir sauka daga mulki, bayan da sojoji suka karbe iko, abinda ya kawo karshen mulkinsa na kusan shekaru 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.