Najeriya

Buhari ya bukaci gaggauta kawo karshen rikicin Tibi da Jukun

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ng.gov.jpg

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin jihar Benue da Taraba su gaggauta kawo karshen rikicin kabilancin da ke faruwa tsakanin Tibi da Jukun, dadadden rikici da ke ci gaba da haddasa asarar rayuka a kasarmai fama da ayyukan ta’addanci Boko Haram baya ga hare-haren ‘yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.

Talla

Umarnin na shugaba Muhammadu Buhari na zuwa a daidai lokacin da rikici tsakanin kabilun biyu ya zafafa, inda ma a ranar Larabar makon da ya gabata aka yi wa wani fada na Majami'ar Katolika, Reverend Father David Tanko kisar gilla.

Wasu gungun mahara ne da ba a tantance ko su wanene ba suka yi wa fadan kwanton-bauna a kauyen Kufai Amadu da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba, suka cinna wa gawarsa da motarsa wuta.

A wata sanarwa daga fadar shugaban kasar na Najeriya, shugaba Buhari ya bukaci sarakunan gargajiya na kabilun biyu, wato sarkin Tibi Tor Tiv, da Aku Uka na wukari da shugabannin addini, da na al’umma a jihohin Binuwai da Taraba da su kira wani taro da zummar kawo karshen wannan rikicin da ya zame wa al’ummomin biyu karfen kafa, inda ya ce babu wani ci gaba da za a samu a yanayi na rikici.

Bayanai sun nuna cewa wannan rikici tsakanin Tibi da Jukun ya faro ne tun a shekarar 1959, yasake faruwa a 1980, da 1990 da kuma shekarar 2001, sai kuma wannan shekarar.

Akalla rayuka 600 ne suka salawanta, tare da asarar kadarori na miliyoyin nairori; sannan mutane da dama daga dukannin bangarorin suka arce daga gidajensu, suka bar sana’o’insu a ‘yan watannin nan sakamakon wannan rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.