Kotu ta aike da sojin Burkina Faso gidan kaso kan juyin mulkin 2015

Wata Kotun soji a birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso ta yankewa wasu janar din soji biyu Gilbert Diendere da Jibril Basole daurin shekaru 10 zuwa 20 a gidan yari bayan tabbatuwar hannunsu a yunkurin juyin mulkin kasar da bai yi nasara ba a shekarar 2015.

Laftal Kanal Yacouba Isaac Zida shugaban Hafson sojin Burkina Faso
Laftal Kanal Yacouba Isaac Zida shugaban Hafson sojin Burkina Faso Reuters/路透社
Talla

A zaman sauraren karar da kotun sojin ta karkare a yau Litinin ta yankewa janar Gilbert Diendéré, shugaban zaratan sojin da ke gadin fadar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore hukuncin zaman wakafi na shekaru 20, bayan da ta kamashi da laifin kisa da kuma barazana ga tsaron kasa, yayin da ta daure janar Djibril Bassole, tsohon Ministan harkokin wajen kasar shekaru 10 a gidan kaso bisa laifin cin amanar kasa.

Kotun ta yi kuma daurin shekaru 19 zuwa 15 ga daukacin sojojin da suka tsare mambobin gwamnatin rikon kwarya na wancan lokaci a kokarin kifar da su.

Sai kuma laftanal kanal Mamadu Bambe da ya sanar da juyin mulki kai tsaye ta kafar talabijin din kasar, ya sha daurin shekaru 10, amma biyar ne zai yi a tsare.

Ranar 16 ga watan Satumbar shekarar 2015, ne ‘yan kwanaki bayan da zanga-zangar gama gari ta kifar da gwamnatin shugaba Blaise Compaore, da ya share shekaru 27 yana jagorantar kasar, gungun dakarun Burkina Faso da ke tsaron fadar shugaban kasa, suka yi yunkurin juyin mulkin ta hanyar kame mambobin gwamnatin rikon kwarya na wancan lokaci, lamarin da ya hallaka mutane 14 tare da jikkata wasu akalla 270.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI