Isa ga babban shafi
Najeriya-Afrika ta kudu

Hakurinmu ya kare kan kisan 'Yan Najeriya a Afrika ta kudu- Gwamnati

Shugaban Nanjeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa bayan hare-haren kin jinin baki kan 'yan Najeriya a birnin Johannesburge
Shugaban Nanjeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa bayan hare-haren kin jinin baki kan 'yan Najeriya a birnin Johannesburge Pulse
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Gwamnatin Najeriya ta ce hakurin ta ya kare kan irin hare haren da Yan Afirka ta kudu ke kaiwa kan yan kasar ta dake zama acan, inda suke kona masu shaguna da kuma sace kayayyaki.

Talla

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya bayyana haka a sakon da ya aike ta kafar twitter inda yake cewa kasar ba zata lamuncewa yadda wasu bata gari ke kai hari kan yan kasar ba.

Wannan mataki ya biyo bayan harin da aka kaiwa Yan Najeriya a karshen mako inda aka kasha 3 daga cikin su, kana aka kona shagunan su a unguwar Jeppestown dake Johannesburg.

Ko a makon jiya yayin wata Kebantacciyar ganawa tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu sai da shugabannin biyu suka tabo batun hare-haren tare da lalubo hanyoyin magance su.

A lokuta da dama dai Cyril Ramaphosa na nuna damuwa da kisan 'yan Najeriyar a kasarsa musamman yayin ganawarsa da Buhari ko kuma da manema labarai.

A cewar shugaban 'Yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta kudun, Adetola Olubajo akwai wata kungiyar bata-gari da ake kira ‘Zulu Dwellers’ ita ke da alhakin kai hare haren kan shaguna da wuraren sana’ar bakin musamman 'yan Najeriya.

Yanzu haka dai tuni gwamnatin Najeriya ta yi sammacin Jakadan Afrika ta kudun a Abuja don yi mata bayani kan matakan da su ke dauka kan kisa da cin zarafin 'yan Najeriyar a kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.