Isa ga babban shafi
Mozambique

Fafaroma Francis ya fara ziyara a kasashen Afrika

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis a babban birnin Maputo na Mozambique
Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis a babban birnin Maputo na Mozambique REUTERS/Mike Hutchings
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis da ya fara cikakkiyar ziyara a kasashen Afrika a wannan Alhamis, ya jinjina wa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Mozambique da ‘yan tawayen kasar, yayinda ya nuna goyon bayansa ga mutanen da ibtila’in guguwa ta shafa a kasar.

Talla

Zaiyarar na zuwa ne bayan gwamnatin kasar ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da tsohuwar kungiyar ‘yan tawayen Renamo wadda ta rikide ta koma babbar jam’iyyar adawa a kasar.

Yakin basasar tsawon shekaru 16 ya daidaita Mozambique wadda kasar Portugal ta yi wa mulkin mallaka.

A yayin ganawa da shugaban kasar Filipe Nyusi, Fafaroma Francis ya jaddada godiyarsa ta kashin kansa kan kokarin da aka yi na samar da zaman lafiya a kasar, yana mai cewa, ta hanyar sasantawa ce kawai za a iya shawo kan duk wani kalubale.

Shugaban jam’iyyar Renamo, Ossufo Momade da sauran shugabannin jam’iyyun adawa na cikin mahalarta ganawar da Fafaroman ya yi da shugaban kasar ta Mozambique.

Ziyarar Fafaroman na zuwa ne bayan Mozambique ta fuskanci ibtila’in guguwar Idai da Kenneth, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 600 tare da jefa dubban jama’a cikin halin kuncin rayuwa.

A karon farko kenan da wani Fafaroma ke ziyartar Mozambique tun bayan ziyarar da Fafaroma John Paul na II ya kai a shekarar 1988, yayinda ake sa ran isarsa kasashen Mauritius da Madagascar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.