kamaru

Kotun soji a Kamaru za ta fara shari'ar jagoran 'yan adawa

Maurice Kamto yayin wani taron manema labarai a Younde
Maurice Kamto yayin wani taron manema labarai a Younde REUTERS/Zohra Bensemra

Hukumomi a Kamaru sun ce ranar juma’a mai zuwa kotun soji zata fara yiwa shugaban Yan adawa Maurice Kamto shari’a duk da korafe korafen da kasashen duniya ke yi.

Talla

Kamto tare da tarin magoya bayan san a fuskantar tuhumar bore da cin amanar kasa, laifuffukan dake dauke da hukuncin kisa.

Wannan shari’ar tana zuwa ne a daidai lokacin da kasashe irin su Faransa da Amurka da kungiyar kasashen Turai suka bukaci sakin shugaba Yan adawan wanda ya kwashe watanni 8 a tsare.

A watan Maris da ya gabata, Mataimakin Sakatren harkokin wajen Amurka, Tibor Nagy da ya ziyarci Kamaru ya bukaci sakin Kamto wanda ya danganta tsare shi da siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.