Lamarin zamba ta intanet ya ta'azzara a Najeriya

A yayin da hukumar yaki da almundahanar kudi da tattalin arziki ta Najeriya EFCC ta kara zage dantse wajen kamen ‘yan damfara da zamba ta intanet a kasar, wanda aka fi sani da Yahoo-Yahoo lamarin sai kara daukar hankali yake musamman ma saboda cikin wanda aka damken harda wasu dama hukumar FBI na Amurka ke nema.Munin wannan lamari da ya zama ruwan dare gama duniya babbar barazana ce ga mutuncin Najeriya a idon duniya.Ya zuwa yanzu EFCC tayi kame a garuruwan Ilori,Legas,Enugu da wasu manyan biranen kasar.Ga rahoton da wakilin mu na Abuja Mohammed Sani Abubakar ya hada mana.

Talla

CORRESPONDENT-MUHAMMAD SANI ABUBAKAR-3.30sec-2019-09-06

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.