Shugaban yan adawar Kamaru zai sake bayyana kotu
Wallafawa ranar:
Yau juma’a jagoran ‘yan adawar Kamaru Maurice Kamto wanda ya zo na biyu a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a shekarar 2018, zai fuskantar shari’a a kotun sojin kasar kan zargin sa da haddasa tashin hankali a wasu yankunan kasar ta Kamaru.
Kasashen duniya da suka hada da Faransa,Amurka da kungiyar kasashen Turai sun bukaci a sako Shugaban yan adawar Maurice Kamto daga kurkukun da ake tsare da shi.
Gwamnatin Kamaru ta yi watsi da kiraye-kiraye kasashen Duniya na ganin ta sako Maurice Kamto , har ila yau magoya bayan sa da dama ke tsare biyo bayan samun su da laifin gudanar da zanga-zanga ba bisa ka’ida ba.
Maurice Kamto ya kuma yi watsi da sakamakon zaben kasar,zaben da hukumar zabe ta ayana Shugaba Paul Biya a matsayin mutumen da ya lashe shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu