Isa ga babban shafi
Najeriya-Afrika ta Kudu

'Yan Najeriya 400 za su dawo daga Afrika ta Kudu

Yadda ake ragargazar 'yan Najeriya a Afrika ta Kudu
Yadda ake ragargazar 'yan Najeriya a Afrika ta Kudu ibtimes.co.uk
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
1 min

Akalla 'yan Najeriya 400 suka sanya sunayensu cikin jerin wadanda suke bukatar gwamnatin kasar ta kwaso su daga Afrika ta Kudu domin mayar da su gida sakamakon munanan hare-haren da ake kai wa baki 'yan kasashen waje.

Talla

Jakadan Najeriya a Johannesburg, Godwin Adama ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Kasar, yayinda kamfanin sufurin jiragen saman Air Peace ya bayyana aniyarsa ta kwaso su zuwa gida.

Jakadan ya ce, daga ranar Laraba mai zuwa, za a fara kwashe 'yan Najeriyan, kuma wadanda basu da takardu, gwamnati ta bada umurnin yi musu cikin gaggawa.

Shi ma shugaban 'yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudu, Ben Okoli ya tabbatar da shirin kwashe masu bukatar komawa gidan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.