Harin ta'addanci ya hallaka mutane 29 a Burkina Faso

Wasu jami'an tsaron Burkina Faso
Wasu jami'an tsaron Burkina Faso AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO

Akalla mutane 29 kawo yanzu aka tabbatar da sun mutu a wasu tagwayen hare-haren ta’addanci da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai yankin arewacin kasar Burkina Faso a yammacin jiya Lahadi.

Talla

Sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta fitar a yau, ta nuna cewa mayakan sun dasa bom a jikin wata motar dakon kaya da mutane a yankin Barsalogho inda kuma nan ta ke ta kashe mutane 15.

Acewar sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin fadar shugaban kasar Burkina Faso Remis Filgance Dandjinou galibin wadanda suka rasa rayukansu ‘yan kasuwa ne dake kan hanyar dawowa daga safara.

Ka zalika sanarwar ta bayyana hari na biyu a yanki mai tazarar kilomita 50 daga inda mayakan suka kaddamar da na farko, inda a nan kuma suka bude wuta kan mutane 14 wadanda suma nan take suka rasa rayukansu.

Wata majiya ta bayyana cewa dukkanin mutane 14 da suka rasa rayukansu a harin na biyu, direbobin motocin da ke safarar abinci zuwa yankin da aka tsugunar da ‘yan gudun hijira ne.

Tun a shekarar 2015 ne Burkina Faso wadda ta fuskanci mulkin mallaka daga Faransa ke fuskantar ayyukan ta’addanci wanda kuma kawo yanzu ya hallaka fiye da mutane 500 baya ga dubbai da suka kauracewa muhallansu.

Ko a makon jiya makamancin harin ya hallaka sojin kasar 24.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.