Tarayyar Afirka

Rwanda za ta karbi bakin - haure daga Libya

Paul Kagame, shugaban Rwanda
Paul Kagame, shugaban Rwanda SIMON MAINA/AFP

Gwamnatin Rwanda ta amince ta karbi daruruwan bakin da suka makale a Libya a karkashin wata yarjejeniya da kasar ta kulla da kungiyar kasashen Afirka ta AU.

Talla

Jakadan Rwanda a kungiyar kasashen Afirka, Hope Tumukunde ya bayyana shirin bayan sanya hannu akan yarjejeniyar tare da wakilan kungiyar AU da na hukumar Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Sanarwar tace tawaga ta farko ta bakin da za’a kwashe sun fito ne daga Yankin Arewacin Afirka, inda za’a kai su wani sansanin kafin sake tsugunar da su.

Majalisar Dinkin Duniya tace baki sama da 42,000 suka makale a Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.