Afrika

Gawar Mugabe na kan hanyar zuwa Zimbabwe

Marigayi Robert Mugabe na kasar Zimbabwe
Marigayi Robert Mugabe na kasar Zimbabwe AFP/Jekesai Njikizana

A yau laraba, wakilai gwamnati da na ‘yan uwan tsohon Shugaban marigayi Robert Mugabe, sun dauko gawar tsohon shugaban daga Singapore zuwa birnin Harare domin yi mata jana’iza.

Talla

Marigayi Robert Gabriel Mugabe wanda aka haifa a yankin Kutama, na kudancin Rhodesia (kasar Zimbabwe a yanzu) ranar 21 ga watan Fabarairun 1924 ya yi kaurin suna ne sanadiyyar kakkarfar kiyayyar da ya nuna ga turawan mulkin mallaka bayan gwagwarmayarsa ta neman ‘yanci.

Haihuwar Mugabe ta zo ne watanni kalilan bayan komawar yankinsu karkashin kulawar Birtaniya matakin da ya tilasta takaitawa al’ummar yankin matakin karatu baya ga ayyukan yi.

Mahaifin Mugabe wanda kafinta ne, ya bar kasar zuwa Afrika ta kudu don gudanar da wasu ayyuka amma bai dawo ba, matakin da ya sanya mahifiyarsa wadda malamar makaranta ce daukar nauyin dawainiyarsa da sauran ‘yan uwansa 3 ta fuskar karatu da ciyarwa ko da dai tun a wancan lokaci Robert Mugabe kan yi sana'ar kiwo don samun kudi.

Karkashin tsarin Birtaniya a Yankin na kudancin Rhodesia da ke matsayin Zimbabwe a yanzu, al’ummar yankin na da zarafin koyon harshen turanci ne kawai amma Mugabe ya samu zarafin halartar makarantar mabiya addinin Kirista da ke yawon yada addini ta O’Hea, inda kuma ya samu cikakken ilimi.

Bayan gano hazakarsa da Malaman makarantar ta O'Hea suka yi ne, suka bashi cikakken horon shekaru 9 da ya bashi damar zama malami a makarantar kafin daga bisani ya tafi Jami'ar Fort Hare da ke kasar Afrika ta kudu inda ya yi digiri a sashen turancin Ingilishi da Tarihi a shekarar 1951 daga nan ne kuma ya koma kasarsa don ci gaba da koyarwa kafin daga bisani a shekarar 1953 ya sake samun digiri a sashen koyarwa karkashin tsarin karatu daga gida.

A shekarar 1955 Mugabe ya koma Arewacin Rhodesia, inda ya yi wani horo na shekaru 4 a kwalejin Chalimbana dai dai wannan lokacin kuma yana ci gaba da karatun digirinsa a bangaren tattalin arziki da jami’ar London shima dai karkashin tsarin karatu daga gida, inda ya kammala a shekarar 1958 bayan komawarsa Ghana.

Mugabe ya kuma yi karatu a kwalejin horar da malamai ta St. Mary inda a nan ne ma ya hadu da matarsa suka kuma yi aure a shekarar 1961.

Mugabe wanda ya rasu yana da shekaru 95 a duniya, bayan isa da gawarsa a birnin birnin na Harare, za a bai wa jama’a damar yi mata ban-kwanan karshe a ranar alhamis da kuma juma’a kafin daga bisani a gudanar da jana’izarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.