Afrika

Najeriya zata fara kwashe yan kasar ta daga Afrika ta kudu

Daya daga cikin jitagen kamfanin Air Peace da ya samu isa Afrika ta kudu
Daya daga cikin jitagen kamfanin Air Peace da ya samu isa Afrika ta kudu Getty Images

Yau Laraba aka fara aikin kwashe ‘yan Najeriya sama da 300 zuwa gida daga Afirka ta Kudu, bayan tarzomar nuni kyamar baki da ake yi a kasar. Kamfanin Air Peace ne ya ce zai bayar da jiragensa kyauta domin dawo da wadanda ke bukata.

Talla

A kasar ta Afrika ta Kudu, an ci gaba da kai hare – hare kan ‘yan kasashen waje, musamman ma a birnin Johannesburg.

Hare –haren daren Lahadi sun yi sanadin mutuwar mutane 2 tare da lalata shaguna.

Najeriya ta shirya kwaso ‘yan kasarta su dari 600, daga ranar Laraba, kuma kyauta, ta kamfanin jiragen saman Air Peace.

‘Yan kungiyar kwadago, masu fafutuka da kungiyoyi masu zaman kansu sun fito karara sun bayyana takaicin su da faruwar lamarin da suka ce abin kunya ne, kamar yadda Teboho Mashota na kungiyar lauyoyi masu kare hakkin bil adama ta yi bayani, inda ta ce abin kunya ne a ce bayan shekaru 25 da samun yancin kai muna cikin wannan yanayi….

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.