Najeriya-Afrika ta Kudu

'Yan Najeriya kusan 200 sun iso gida daga Afrika ta Kudu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya bada umurnin a kwaso 'yan Najeriya daga Afrika ta Kudu/ AFP PHOTO / SAUL LOEB
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya bada umurnin a kwaso 'yan Najeriya daga Afrika ta Kudu/ AFP PHOTO / SAUL LOEB AFP/SAUL LOEB

Jirgin farko dauke da ‘yan Najeriya 189 da suka guje wa tarzomar nuna kyamar baki a kasar Afirka ta kudu, ya sauka a birnin Lagos a yammacin jiya laraba.

Talla

Mai taimakawa ta musamman ga shugaban Najeriya a game da lamurran da suka shafi ‘yan kasar da ke zaune a kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa, ta ce da farko an tsara jirgin zai kwaso mutane 317 ne zuwa gida, to sai dai an fuskanci wasu ‘yan matsaloli wajen tantance ‘yan Najeriyar.

Misis Dabiri-Erewa, ta ce an samu jinkiri na tsawon sa’o’i 5 kafin jirgin ya taso daga Johannesburg, inda ta zargi mahukunta a Afirka ta Kudu da kin taimaka wa ‘yan Najeriya a lokacin da ake kokarin samar masu da takardu don ficewa daga kasar.

Lokacin da take jagorantar wadanda suka sauka a birnin Lagos domin rera taken Najeriya, Dabiri-Erewa ta ce gwamnati za ta tallafa wa wadannan mutane, duk da cewa ba ta yi karin bayani a game da irin taimakon da za a ba su ba.

Samson Aliyu, wani dan Najeriya da ya share tsawon shekaru biyu yana sana’ar sayar da tufafi a Johannesburg, wanda ya kasance cikin ayarin farko da suka sauka a filin jirgin saman birnin na Lagos, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa da kyar ya tsira da rayuwarsa, lokacin da matasa suka kai masu farmaki a kasar ta Afirka ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.