Isa ga babban shafi

An rufe yakin neman zabe a Tunisia

Abdel Fattah Mourou, mataimakin shugaban Tunisia, kuma daya daga cikin 'yan takaran shuganacin kasar
Abdel Fattah Mourou, mataimakin shugaban Tunisia, kuma daya daga cikin 'yan takaran shuganacin kasar Wikimedia Commons/Ennahda
Zubin rubutu: Michael Kuduson
2 Minti

A Juma’ar nan ne yan takarar mukamin shugabancin kasar Tunisia ke rufe zazzafan yakin neman zaben da suka gudanar kafin zaben na ranar lahadi mai zuwa dake cike da rashin tabbas.

Talla

A wannan rana ta karshe ga yakin neman zaben ana sa ran kotun daukaka kara ta zartar da hukumci dangane da karar da aka shigar kan Nabil Karoui, daya daga cikin yan takarar, wanda tun ranar 23 ga watan Agustan da ya gabata ya ke rufe a kurkuku sakamakon zarginsa da halatta kudaden haram

Dan kasuwa ne dake yawan caccakar gwamnati inda ya ke zarginta da yin amfani da kotu domin hana shi tsayawa takarar. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ba zai taba janye takarasa a zaben ba, tare da bayyana tsunduma cikin yajin kin cin abinci

Magoya bayansa dai sun yi alkawalin gudanar da zanga zanga a Juma’a a gaban harabar gidan kurkukun Monarguia, yan kilomitoci da Tunis babban birnin kasar ta Tunisiya.

Shahararren titin Bourguiba, dake dauke da fadar shugaban kasar ta Tunisia a duk tsawon ranar Juma’a zai karbi tarurukan karshen na yakin neman zaben mabanbantan jam’iyun siyasar kasar da ya hada da na Abdelfattah Mourou, na jam’iyar da ke da ra’ayin musulunci ta Ennahdha ; da ta M. Karoui da na dan takarar yan gurguzu Hamma Hammami.

A yayinda ake sa ran bangaren Firaminista, Youssef Chahed ya zabi wasu unguwanin Tunis domin rufe yakin neman zabe, sauran yan takarar kuma zasu kammala ne a garuruwan dake cikin kasa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.