Najeriya-Nijar

Kasashen Najeriya Nijar da Chadi za su hada hannu don inganta noma

Matakin dai na da nasaba da kafewar tafkin Chadi wanda ke barazar ga harkokin neman kasashen 3.
Matakin dai na da nasaba da kafewar tafkin Chadi wanda ke barazar ga harkokin neman kasashen 3. RFI/ Julia Cerrone

Kasashen Najeriya da Nijar da kuma Chadi na wani aikin hadin kai da zai inganta yanayin noma a tsakanin kasashen su da kuma farfado da Tafkin Chadi dake cigaba da tsukewa.

Talla

Shugaban hukumar ceto yankunan da rairayi ya mamaye dake Najeriya, Bukar Hassan ya ce tunda matsalar kwararowar hamada bata san iyakokin kasashe ba, ya zama wajibi ga wadannan kasashe dake makotaka da juna suyi aiki tare wajen farfado da harkar noma da shuka itatuwa domin inganta rayuwar mazauna kusa da tafkin Chadi.

Yayin da ya ke jawabi wajen taron muhalli a New Delhi dake India, Hassan ya ce a yau ba’a iya noma a bangaren Najeriya da ke makotaka da tafkin Chadi, ganin yadda akalla kashi 90 na ruwan da ke tafkin ya tsuke.

Jami’in ya ce wannan ya sa hukumomin Najeriya suka kaddamar da shirin fadakar da mazauna jihohi 11 da ke kusa da iyakar da ke fuskantar barazanar kwararowar hamada muhimmanci shuka itatuwa da noman rani domin yaki da matsalar.

Shugaban hukumar yace yanzu haka ana kokarin tara Dal abiliyan 8 daga kasashen Afirka da masu bada agaji da Bankin duniya da kungiyar kasashen Turai domin ganin anyi aikin yashe tafkin da kuma janyo ruwa daga kogin Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.