Jami'an tsaron Congo sun hallaka kwamandan 'yan ta'addan Rwanda

Wasu 'yan tawayen Hutu na Rwanda
Wasu 'yan tawayen Hutu na Rwanda Hector Mata/AFP

Jami’an tsaron Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun sanar da harbe wani babban kwamandan ‘yan tawayen Hutu na kasar Rwanda da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ke nema ruwa a jallo, kan zargin aikata laifukan yaki.Tuni hukumomin Rwanda suka yaba da matakin wanda suka kira labari mai dadi ga zaman lafiyar yankin.

Talla

Kakakin ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Janar Leon-Richard Kasonga, ya ce, a daren Talata sojojin su ka harbe Sylvestre Mudacumura, kwamadan kungiyar ‘yan tawayen Rwanda ta FDLR a yankin arewacin Kivu.

Tuni dai mahukuntan Rwanda, suka nuna farin cikin su dangane da kisan Sylvestre Mudacumura da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo, kan rawar da ya taka a kashe-kashen Rwanda da Congo, da suka hada da fyade, da azabtarwa.

A cewar Ministan harkokin wajen Rwanda Olivier Nduhun-girehe, wannan mataki na tabbatar da kokarin gwamnatin shugaba, Felix Tshisekedi na Congon game da yaki da miyagun masu dauke da makamai.

Ministan harkokin wajen na Rwanda ya kuma bayyana cewa, mutuwar Mudacumura labari ne mai dadi, ga zaman lafiya da tsaron kasashen yankin.

Majalisar dinkin duniya ta ce, kungiyar tawayen Hutu nada kimanin mayaka 500 zuwa 600, a yankin arewa da kudancin kivu da ma kudancin Katanga, mai arzikin ma’adaina a Jamhuriyar dimokradiyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.