Isa ga babban shafi
Masar

Jami'an tsaron Masar sun kame masu zanga-zangar adawa da al-Sisi

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi. AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Jami’an tsaron Masar sun kame mutane da dama, da suka shiga wata zanga-zangar adawa da shugaban kasar Abdel Fattah Al Sisi a jiya Juma’a.

Talla

An dai soma zanga-zangar ce a filin Tahrir, inda ya zama cibiyar juyin juya halin da ya kawo karshen mulkin shugaba Hosni Mubarak.

Wani da ya shaida yadda abin ya faru, ya ce ba a jima da soma zanga-zangar ba ‘yan sandan dake cikin damara da taimakon masu farin kaya suka damke gungun masu zanga-zangar.

Tun a shekarar 2013 gwamnatin soji ta shugaba Al Sisi da ta kawar da shugabancin marigayi Muhd Morsi, ta haramta irin wannan zanga-zanga ta kin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.