Jamhuriyar Congo

Za a soma raba sabon nau'in rigakafin Ebola a Congo

Wasu jami'an lafiya a Jamhuriyar Congo, yayin baiwa mutane rigakafin cutar Ebola.
Wasu jami'an lafiya a Jamhuriyar Congo, yayin baiwa mutane rigakafin cutar Ebola. Augustin WAMENYA / AFP

Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Congo, sun bayyana shirin soma amfani da wani sabon nau’in maganin rigakafin cutar Ebola, wanda kamfannin sarrafa magunguna na J&J ya samar.

Talla

Kawo yanzu dai, tawagar jami’an lafiyar dake sa ido kan yakar annobar ta Ebola a Jamhuriyar Congon, basu bayyana lokacin da za’a soma baiwa jama’a sabon maganin rigakafin ba, wanda ke zama kari, kan maganin rigakafin Ebola na farko da kamfanin Merck ya samar, wanda zuwa yanzu aka baiwa sama da mutane dubu 225.

An dai kwashe tsawon lokaci ana tafka muhawara tsakanin jami’an lafiya a Congo, kan sabon maganin na kamfanin J&J, wanda tsohon ministan lafiyar kasar Ilunga Kalenga yaki amincewa a soma amfani da shi, saboda rashin tabbas kan sahihancinsa.

Sai dai tawagar yanzu dake aikin yakar annobar ta Ebola a jamhuriyar ta Congo, ta ce maganin bashi da wata illa, domin tuni aka soma amfani da shi, a kasashen Uganda da kuma Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.