Isa ga babban shafi

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da al-Sisi

Wasu jami'an tsaro lokacin da su ke tarwatsa masu zanga-zanga
Wasu jami'an tsaro lokacin da su ke tarwatsa masu zanga-zanga MOHAMED EL-SHAHED / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Jami'an tsaro a Masar sun yi arangama da daruruwan masu zanga zangar adawa da shugaba Abdel Fatah al Sisi a birnin Suez a karshen mako, inda suka harba musu hayaki mai sa hawaye da harsashin roba.

Talla

Rahotanni sun ce wannan yasa aka jibge jami’an tsaro a Dandalin Tahrir, fitaccen wurin da ya zama dandalin gudanar da zanga zangar shekarar 2011 wadda tayi sanadiyar raba shugaba Hosni Mubarak da kujerar sa.

Hauhawar farashin kayan masarufi da kuma shirin tsuke bakin aljihun gwamnati kasar ta Masar bisa shawarar asusun ba da lamuni na duniya IMF, sun jefa al’ummar kasar cikin halin kuncin rayuwa.

Alkaluma sun bayyana cewar, mutum guda daga cikin 3 na 'yan kasar na fama da matsanancin talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.