Isa ga babban shafi
Duniya

Jawabin Shugaba Buhari a Majalisar Diunkin Duniya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake gabatar da bukatar yashe tafkin Chadi wanda matsalar sauyin yanayi ta sa shi yake cigaba da tsukewa da kuma illa ga mutane akalla miliyan 40 da suka dogara da shi wajen noma da kamun kifi.

Talla

Shugaba Buhari yace wadannan mutane miliyan 40 na bukatar shugabannin kasashen duniya dake halartar taron muhalli da suyi nazari kan halin da suke ciki domin daukar matsayin warware matsalar.

Shugaban yace Najeriya zata cigaba da hadin kai da kasashen duniya wajen dawo martabar tafkin domin inganta rayuwar jama’ar dake kewaye da shi da kuma samar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.