FIFA

Messi gwarzon shekara na FIFA

Lionel Messi na karbar kyautar dan wasan Fifa na shekarar 2019 a Milan
Lionel Messi na karbar kyautar dan wasan Fifa na shekarar 2019 a Milan REUTERS/Flavio Lo Scalzo

A birnin Milan na kasar Italiya dan wasan Barcalona dan asalin Argentina Lionnel Messi ya lashe kyautar dan wasan shekara na Fifa 2019.

Talla

Masu zabe sun bayyana zabin zuwa dan wasan fiye da Ronaldo ,da kuma Virgil Van Dijk dan wasan da akasarin manazarta kwallon kafa suka fi mayar da hankali ,kasancewar shine ya lashe kofin zakarun Turai da kungiyar sa ta Liverpool,ya samu buga wasar karshe ta cin kofin nahiyoyin da kungiyar Netherlands ,wanda ya kuma lashe kofin fitaccen dan wasan Turai.

Lionnel Messi wanda ya zura kwallaye 36 a wasani 34,wannan dai ne karo na 6 da ya lashe wannan kyauta.

A bangaren mata yar wasar Amurka Megan Rapince ce ta lashe kyautar yar wasar shekara ta Fifa.

Megan ta taka gaggarumar rawa a gasar cin kofin Duniya da ta gudana a Faransa.

Bangaren mai tsaron gida, hukumar Fifa ta baiwa Alisson Becker mai tsaron gidan kungiyar Liverpool wanda ya yiwa Ederson na Manchester City da Marc Andre Ter Stegen kashin mumuke kyautar mai tsaron gida na shekarar nan.

Bangaren mata yar kasar Netherlands Van Veenendaal ce ta lashe kyautar maiu tsaron gida na wannan shekara.

A bikin da ya gudana a birnin Milan na kasar Italiya Fifa ta ware kyautar mai horo da ya nuna gwaninta na wannan shekara zuwa Jurgen Klopp dan kasar Jamus mai horar da kungiya ta Liverpool,Klopp ne yam aye gurbin Didier Deschamps bafaranshe da ya lashe kyautar shekarar da ta gabata.

Akasarin manazarta wasannin kwallon kafa sun sa ran cewa Pep Guardiola dake horar da kungiyar Manchesterd City ne zai lashe wannan kyauta,yayinda wasu suka bayyana zabin su zuwa Mauricio Pochenttino mai horar da kungiyar Tottenham a Ingila.

Wasu daga cikin manyan yan wasa da suka hada da Samuel Eto’o sun bayyana fatan sun a ganin an dama da yan wasan Afrika.

Samuel Eto’o ya bayyana cewa yan lokuta kafin an soma bayyana sunayen yan wasa da suka lashe kyuaututuka, Mahamad Salah ko Sadio Mane za su kasance daga cikin yan wasa da Fifa za ta yaba da su.

A karshe mu leka zuwa akwatin zabe da aka kada don zaben dan wasan shekara na Fifa:

Virgil Van Dijk ya samu kashi 24 cikin dari na kuri’u,

Cristiano Ronaldo da bai samu halartar wannan bikin bay a tashi da kashi 21 cikin dari na kuri’u yayinda gwarzon shekara Lionnel Messi ya samu kashi 55 cikin dari na kuri’u masu zabe gwarzon dan Wasan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.