Isa ga babban shafi
Najeriya-Afrika

Ina fatan yiwa al'umma hidima tamkar Bill Gates - Dangote

Hamshakin attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote.
Hamshakin attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote. AFP/Stéphane de Sakutin
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 Minti

Hamshakin attajirin nahiyar Afrika dan Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya ce fatansa a kullum shi ne cimma burin ware sashin dukiyarsa mai tsoka wajen yiwa al’umma hidima, tamkar yadda hamshakin attajirin duniya Bill Gates ke yi.

Talla

Dangote ya bayyana burinsa ne, yayin halartar wani taro da gidauniyar Bill and Melinda Gates ta shirya a birnin New York, dake maida hankali kan bibiyar halin da ake ciki kan kokarin da kasashe da sauran hukumomi ke yi na cimma muradun karni.

Hamshakin attajirin na nahiyar Afrika ya ce har kullum Bill Gates yana burge shi, gami da bashi mamaki, la’akari da yadda a matsayinshi na dan kasar Amurka, yake matukar kaunar nahiyar Afrika, musamman ‘yan Najeriya, tare da ci gaba da baiwa al’ummar kasar tallafin biliyoyin daloli duk dacewa bashi da alaka da su.

Alhaji Aliko Dangote, ya haduwa da Bill Gates ya taimaka masa masa matuka, wajen fahimtar tarin kalubalen da Najeriya ke fuskanta a fannonin da dama ciki harda lafiya da tattalin arziki.

A baya bayan nan hamshakin attajirin na nahiyar Afrika, ya soma shirin rabawa mata akalla dubu dari da shidda a sassan Najeriya tallafin naira biliyan daya da miliyan dari.

Jaridar Daily Trust dake Najeriyar ta rawaito cewa, gidauniyar bada tallafin attajirin ta soma aikin tantance matan da suka cancanci karbar tallafin jarin sana’o’in a wasu jihohin arewacin kasar.

Jihohin kuwa da za su amfana da tallafin sun hada da Sokoto, inda adadin mata kimanin dubu 23,000 za su amfana, sai Katsina inda mata dubu 34 za su amfana, sai kuma jihohin Kebbi da Zamfara, inda adadin matan dubu 21 da dubu 28 za su amfana.

Wannan yunkuri dai ci gaba ne da aiwatar da shirin tallafawa ‘yan Najeriya miliyan 1 da attajiri Dangote ya kaddamar a Kano cikin shekarar 2011, wanda zai shafi dukkanin sassan Najeriya.

Zuwa yanzu kuma kididdiga ta nuna cewar mata da matasa dubu 300 da doriya suka amfana da shirin tallafin a jihohin Kano, Kogi, Jigawa, Adamawa da kuma Yobe. Sai kuma jihohin Legas, Nasarawa, Niger da kuma Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.