Chadi

Mahakan zinare 52 sun rasa rayukansu a Chadi

Ramin hakar zinare ya rubza kan mutane a Chadi.
Ramin hakar zinare ya rubza kan mutane a Chadi. The Independent Uganda

Adadin mutanen da suka halaka a arewacin Chadi ya karu zuwa 52, sakamakon rubzawar wani ramin hakar zinare, yayinda suke tsaka da aiki, inda har yanzu jami’an ceto ke laluben wasu mahakan da dama da suka bace.

Talla

Da fari dai jami’an ceto a kasar ta Chadi sun ce mutane 30 suka halaka, a lokacin da hadarin ya auku a yankin Kouri Bougoudi dake lardin Tibesti, a ranar talatar da ta gabata.

Kawo lokacin wallafa wannan labari dai, adadin wadanda suka jikkata ya tsaya a 37, kuma 21 daga cikinsu na cikin mummunan yanayi.

A baya bayan nan dai lardin Tibesti ya zama matattarar kungiyoyi masu dauke da makamai, da kuma gungun masu fasakauri dake sata ko hakar zinare ba bisa ka’ida ba.

A watan Janairu wani kazamin rikici tsakanin larabawan Libya mahakan zinare da kuma mahakan kabilar Ouaddai dake kasar ta Chadi, ya haddasa hasarar gwamman rayuka, lardin na Tibesti.

Chadi na daga cikin kasashen Sahel masu fama da matsalolin tsaro ta fuskoki da dama, da suka hada da barzanar mayakan Boko Haram, ‘Yan tawaye da kuma wasu kananan kungiyoyin sa kai masu dauke da makamai, sai kuma rikicin kabilanci da kuma tsakanin manoma da makiyaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.