Burkina Faso

'Yan bindiga sun hallaka fararen hula 8 a Burkina Faso

Jami'an tsaro a yankin da harin ya faru
Jami'an tsaro a yankin da harin ya faru ISSOUF SANOGO / AFP

Akalla fararen hula 8 aka tabbatar da mutuwarsu bayan harin wasu ‘yan ta’adda haye akan babura ciki wani kauye da ke yankin arewacin Burkina Faso mai fama da hare-hare ‘yan bindiga baya ga mayaka masu ikirarin jihadi.

Talla

Rahotanni sun bayyana cewa da safiyar yau Asabar ne, Maharan su kusan 20 suka rufarwa kauyen Komsilga da ke yankin Zimtanga inda suka bude wutan kan fararen hula tare da hallaka mutanen 8 yayinda wani mutum guda kuma ya bace.

Wasu ganau sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, Maharan sun kuma kone shagunan kasuwanci tare da ababen hawan jama’a, yayinda wani ya bayyana cewa Maharan sun kuma awon gaba da wasu fararen hula da bai bayyana adadinsu ba.

Tuni dai gwamnatin Burkina Faso ta aike da jami’an tsaro yankin don bin sahun Maharan tare da ceto mutanen da suka sace.

Ko a makon jiya dai makamancin harin ya hallaka fararen hula 9 ciki har da ‘yan kasuwar da ke dawowa daga fatauci.

Rahotanni sun bayyana cewa daga shekarar 2015 zuwa yanzu akalla fararen hula 580 makamantan hare-haren ya hallaka a kasar ta Burkina Faso mai fama da hare-haren ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.