Buhari zai ziyarci Afrika ta kudu bayan tsamin alaka tsakanita da Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta kudu Cyril Ramphosa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta kudu Cyril Ramphosa. Pulse

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Afrika ta kudu a gobe Laraba, bayan gayyatar da ya samu daga takwaransa  Cyril Ramaphosa duk dai dangane da dambarwar kisan 'yan Najeriya a kasar wadda ke neman haddasa tsamin alaka tsakanin kasashen biyu.

Talla

Sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban Najeriyar Garba Shehu ya fitar ta ce yayin ziyarar Buhari zai gana da 'yan Najeriya mazauna Afrika ta kudun don tattaunawa game da matsalolin da su ke fuskanta baya ga karfafa musu gwiwa kan irin matakan da gwamnati ke dauka don basu kariya.

Sanarwar ta bayyana cewa Buhari da Ramaphosa za su jagoranci taron hulda tsakanin kassahen biyu wanda zai kunshi manyan 'yan kasuwa da masu zuba jari kana a karshe za su gabatar da takardar bayan taro ga manema labarai.

Cikin wadanda za su raka shugaban har da Gwamnonin jihohin Kano da Pulato da Ebonyi baya ga ministocin Najeriyar 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.