Tanzania-Burundi

Burundi za ta fara aikin kwashe 'yan gudun hijirarta daga Tanzania

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Burundi da ke samun mafaka a sansanin Tanzania
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Burundi da ke samun mafaka a sansanin Tanzania PHOTO | AFP

Gwamnatin Burundi ta sanar da fara aikin kwashe al’ummarta da ke gudun hijira a Tanzania wadanda za ta kwashe bisa tsarin rukuni-rukuni karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma a baya-bayan nan.

Talla

Wani babban Jami’in gwamnatin Burundi Nestor Bimenyimana da ke matsayin jagoran aikin kwaso ‘yan gudun hijirar daga Tanzania, ya ce a jibi alhamis ne rukunin farko da ya kunshi ‘yan gudun hijira dubu guda za su baro Tanzania don dawowa gida.

Cikin watan Agustan da ya gabata ne, gwamnatocin kasashen Burundi da Tanzania suka cimma yarjejeniyar fara aikin kwashe ‘yan gudun hijirar su fiye da dubu dari 2 da ke samun mafaka a Tanzania wanda aka alkwarta farawa a ranar 1 ga watan Octoba wato yau Talata.

Aikin kwashe ‘yan gudun hijirar wanda gwamnatin Burundi ta bayyana cewa zai gudana ne kyauta, kungiyoyin kare hakkin dan adam baya ga Majalisar dinkin duniya na diga ayar tambaya game da shirin, wanda su ke ganin wani yunkuri ne na tilastawa mutanen komawa gida don ci gaba da fuskantar azabtarwa.

Babar Baloch shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce a halin da Burundi ke ciki, babu bukatar kwashe tarin ‘yan gudun hijira wadanda ke zaune cikin salama a Tanzania.

Fiye da ‘yan gudun hijira dubu dari 4 ne, suka tsere daga Burundi zuwa kasashen Tanzania Rwanda da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, bayan rikicin da ya biyo bayan takarar shugaba Pierre Nkurunziza a zaben 2015 wadda ta kai ga kisan dubun nan fararen hula.

Majalisar dinkin duniya dai na ganin akwai bukatar bai wa ‘yan gudun hijirar zabin zama a Tanzania ko kuma komawa gida kafin fara aikin kwashesu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.