kamaru

An dakatar da shari'ar da ake yi wa 'yan awaren Kamaru

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya AFP

Shugaban Kamaru Paul Biya ya ba da umurnin dakatar da shari’ar da ake yi wa daruruwan 'yan awaren da ke neman ballewa domin kafa kasarsu a yankin masu magana da Turancin Ingilishi.

Talla

Firaministan kasar Joseph Dion Ngute ya ce, an dauki matakin ne domin kwantar da hankalin al’ummar kasar da rikicin 'yan awaren ya raba kawunansu tare da haddasa asarar dimbin rayuka.

Kungiyar ‘International Crisis Group’ ta ce, mutane kusan 3,000 suka mutu sakamakon rikicin, yayin da sama da 500,000 suka tsere wa gidajensu, sannan wasu suka zama 'yan gudun hijira a kasashe makwabta.

Wannan ya sa shugaba Paul Biya ya shirya taron kasa domin sasanta al’ummar kasar, amma 'yan awaren da kuma 'yan adawa sun kaurace wa taron muhawarar ta kasa.

'Yan adawan sun gindaya sharadin cewa, sai an saki shugabansu, Julius Ayuk Tabe da magoya bayansa da aka yi wa daurin rai da rai kafin su shiga taron.

Mazauna yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi su ke da kashi daya bisa 5 na al’ummar Kamaru mai yawan mutane miliyan 24.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.