Isa ga babban shafi

Kungiyoyin ta'addanci Afrika sun hade don kalubalantar G5 Sahel

Wasu dakarun Sojin hadaka da ke yakar ta'addanci a Burkina Faso
Wasu dakarun Sojin hadaka da ke yakar ta'addanci a Burkina Faso US Army/Richard Bumgardner
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Wasu rahotanni daga Burkina Faso na nuni da cewa kungiyoyin ‘yan bindiga masu ikirarin jihadi da ke kaddamar da hare-haren ta’addanci a yankin sahel sun hade waje guda don kalubalantar matakin kasashen yankin na hada karfi don kakkabe barazanar tsaron da su ke fuskanta daga kungiyoyin.

Talla

A cewar tsohon shugaban ‘yan tawayen Arewa maso gabashin kasar Mali kungiyoyin wadanda suka kunshi Ansar Dine da Front du Macina da al-Mourabitoune dama AQMI baya ga Ansarul Islam da kuma kungiyar ISIS a yankin babbar Sahara, sun hade waje guda tamkar rundunar tsaro ta G5 Sahel mai yaki da ta’addanci a yankin don ci gaba da fadada hare-harensu.

Wasu bayanan sirri sun bayyana cewa wani reshe na kungiyar Macina mai rajin taimakon musulunci a Mali ne ya tallafawa kungiyoyin ta’addanci samun damar kutsa kai Burkina Faso don gudanar da hare-haren ta’addancin karkashin jagorancin kungiyar ISIS a yankin babbar sahara (EIGS).

harin baya bayana nan da aka kai a garin Boulkessi wanda aka dora alhakin kai sa kan dakarun hadakar gungun yan ta’addan a Burkina Faso inda kungiyar Ansarul Islam ke ci gaba da tabbatar da wannan babbar barzana ta hadewar kungiyoyin a cikin kasar ta Burkina Faso.

Wasu rahotanni daga majiyoyin tsaron Burkina faso sun bayyana shakku kan yadda za a ce kungiyar Ansarul Islam kadai ta kaddamar da hare-haren baya-bayan nan da ya hallaka Sojin kasar 25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.