Najeriya-Afrika ta Kudu

Najeriya da Afrika ta Kudu sun karfafa alaka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Najeriya da Afrika ta Kudu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar baiwa ‘yan kasuwa, malamai da dalibai, da sauran masu yawan balaguro tsakanin kasashen takardun Biza da za su shafe shekaru 10 suna aiki.

Talla

An cimma yarjejeniyar ce yayinda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke karkare ziyarar da ya kai kasar Afrika ta Kudun a jiya Juma’a gabannin dawowar shugaban.

Kasashen sun ce daukar matakin bangare ne na karfafa alakar tattalin arziki, siyasa da kuma ala’adu tsakaninsu.

Wasu karin batutuwan da shugabannin na Najeriya da Afrika ta Kudu suka tattauna tare da cimma matsaya akai, yayin ganawarsu a Pretoria, sun hada da musayar bayanan asiri da kuma kaddamar da wani shiri da zai dinga basu damar hango tashin hankali domin daukar matakin gaggawa, abinda zai dakile yiwuwar sake fsukantar matsalar bata gari, ta kashe baki a Afrika ta Kudu.

Cikin watan Satumba shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya aike da jakada na musamman zuwa kasashen Afrika  da suka hada da Najeriya da Nijar da Ghana da Senegal da Tanzania da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da kuma Zambia, domin kwantar musu da hankali kan hare-haren da ake kai wa baki 'yan kasashen da ke zaune a kasar.

Hare-haren kin jinin bakin sun tilastawa 'yan kasashen Zimbabwe da Mozambique tserewa gida yayinda itama Najeriya ta kwashe al'ummarta da ke kasar zuwa gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.