Tanzania

Shugaban Tanzania ya jinjina wa gwamnan da ya yi wa dalibai bulala

Misalin irin sandunan da aka yi amfani da su wajen jibgar daliban
Misalin irin sandunan da aka yi amfani da su wajen jibgar daliban RFI/Hausa

Shugaban Tanzania John Magufuli ya jinjina wa wani gwamnan yanki wadda bulalar da ya yi wa wasu daliban sakandare su 14 ya janyo ceceku, inda ya ce da ya zane su fiye da haka.

Talla

Hotunan bidiyo na wannan al’amari da ya mamaye shafukan sadarwar intanet ya nuna Albert Chalamila, gwamnan yankin Mbeya a arewacin Tanzania yana wa yaran bulala uku – uku, yayin da suke kwance a kasa.

Laifin da suka yi dai na karya dokar makarantar ce, da ta haramta mallakar wayar salula kuma ana zarginsu da kona dakin kwanan su don takaici.

Wannan hukunci da aka aiwatar a gaban takwarorin daliban, ‘yan sanda da malamai ya janyo kakkausar suka a dandalin zumunta dabam – dabam.

Shugaba Magafuli ya ce, "Ina jinjina wa wannan gwamnan da ya zane wadannan dalibai, kuma a gaskiya hukuncin yayi kadan. Da ma ya kara musu".

Shugaban ya umurci gwamnan da ya dakatar da daliban, kuma ya tilasta wa iyayensu biyan barnar da suka yi kafin su koma makarantar, sannan a jefa wadanda ke da hannu kai tsaye kurkuku.

Kundin tsarin mulkin Tanzania na 1979 ya tanadi cewa shugaban makaranta ne kawai ke da ikon aiwatar da hukunci irin wannan ga dalibai, kuma sai idan sun aikata babban laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.