Rwanda

'Yan bindiga sun halaka mutane 8 tare da jikkata 18 a Rwanda

Paul Kagame, shugaban Rwanda
Paul Kagame, shugaban Rwanda RFI/F24

‘Yan sanda sun ce wasu ‘yan bindiga daba a san ko su wanene ba sun bindige mutane 8 har lahira suka kuma jikkata 18 a arewacin Rwanda, kusa da iyaka da Congo daf da wayewar garin Asabar din nan.

Talla

An kai wannan harin ne a garin Musanze, yankin da ke daukan hankalin masu yawon bude ido, saboda wajen shakatawan nan na Volcanoes National Park da tuddan nan mai cike da gogon biri.

Wata sanarwar da ‘yan sandan suka fitar ta ce shida daga cikin mutanen da takobi aka halaka su, yayin da sauran suka mutu ta harbin bindiga.

Da ma kungiyoyin ‘yan tawayen Rwanda dake gudanar da ayyukansu daga jamhuriyar Dimokaradiyar Congo sun sha kai wa yankin hare –hare.

Daga cikin wadannan kungiyoyin akwai Democratic Forces for the Liberation of Rwanda, wanda ‘yan gudun hijiran Hutu a gabashin Congo suka kafa bayan kisan kare – dangi na shekarar 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.