Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Barrister Buhari Yusuf kan takaddamar da ta dabaibaye shirin daukar sabbin 'yan Sanda a Najeriya

Sauti 02:58
Jami'an 'yan sandan Najeriya
Jami'an 'yan sandan Najeriya Daily Post Nigeria

Yanzu haka wata takaddama mai zafi ta kaure tsakanin rundunar 'Yan Sandan Najeriya da kuma Hukumar da ke kula da ayyukan 'Yan Sandan kan wanda ke da alhakin daukar sabbin 'Yan Sanda aiki.Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin daukar sabbin Yan Sanda 10,000 domin cike gibin karancin jami’an tsaron da ake da shi, amma wannan rikici ya dakatar da aikin.Mun yi iya bakin kokarin domin jin ta bakin bangarorin biyu, amma abin yaci tura, sai dai kowanne bangare a bayan fage yana tauna tsakuwa kan lamarin, yayin da aikin daukan sabbin jami’an ya tsaya cik.Dangane da wannan dambarwa mun tattauna da Barr Buhari Yusuf, lauya mai zaman kan sa, kuma ga tsokacin da yayi akai.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.