Isa ga babban shafi
Tunisia

Kotu ta sallami dan takarar shugabancin Tunisia daga gidan Yari

Nabil Karoui dan takarar neman kujerar shugaban kasa a Tunisia da ya zo 2 a zagayen farko, tare da magoya bayansa, bayan sakinsa daga gidan Yari. 9/10/2019.
Nabil Karoui dan takarar neman kujerar shugaban kasa a Tunisia da ya zo 2 a zagayen farko, tare da magoya bayansa, bayan sakinsa daga gidan Yari. 9/10/2019. AFP/ANIS MILI
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Kotun Kolin Tunisia ta sallami dan takarar kujerar shugabancin kasar Nabil Karoui daga gidan Yari, yayin da ya rage kwanaki kalilan a yi zaben shugabancin kasar zagaye na 2, a ranar lahadin nan dake tafe.

Talla

Cikin watan Agustan da ya gabata jami’an tsaro suka kame hamshakin dan kasuwar kafin zagayen farko na zaben shugabancin kasar, abinda ya sa shi shafe tsawon lokacin yakin neman zabe garkame a gidan Yari, bisa zarginsa da aikata laifukan halatta kudaden haramun da kuma kin biyan haraji da gangan, zarge-zargen da ya musanta.

Kan wannan batu ne a makon jiya shugaban Tunisia mai rikon kwarya Muhammad Ennaceur, ya ce tsare Karoui da rashin samun damar yakin neman zabensa, ya nakasa sahihancin zaben shugabancin kasar, yayinda masu sa ido kan zaben suka ce matakin tsare dan takarar ya nun aba a shirya yin adalci ba.

Tuni dai itama, hukumar zaben Tunisian ta yi gargadin cewa, kotu za ta iya soke zaben, muddin Karaoui ya garzaya gare ta, la’akari da cewa an hana shi damar yakin neman zabe.

Yayin zagayen farko na zaben shugabancin kasar ta Tunisia makwanni 3 da suka gabata, Karaoui ya samu kashi 15 da rabi na kuri’un da aka kada, yayinda abokin hamayyarsa Kais Saied farfesa a fannin shari’a ya samu kashi 18 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.