Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Rikici ya raba 'yan Burkina Faso rabin milyan da muhallansu- rahoto

Wasu al'ummar Burkina Faso da rikici ya raba da gidajensu
Wasu al'ummar Burkina Faso da rikici ya raba da gidajensu AFP Photos/ISSOUF SANOGO
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Wani rahoton hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa adadin mutanen da rikici ya raba da muhallansu a Burkina Faso kawo yanzu ya kai rabin miliyan, bayan da adadin masu gujewa rikicin kasar ya karu matuka a watanni ukun baya-bayan nan.

Talla

Kididdigar hukumar ta UNHCR ta nuna cewa kawo yanzu adadin ‘yan kasar Burkina Faso da suka fice daga muhallansu sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga da kungiyoyi masu ikirarin jihadi ya kai dubu dari hudu da 86 inda a iya watanni ukun da suka gabata mutane dubu dari 2 da 67 suka rasa muhallansu.

Cikin bayanan da hukumar ta bayar a yau Juma’a ta nuna cewa yanzu haka ‘yan kasar dubu 16 ne gudun hijira a makota, yayinda adadin mutane miliyan guda da rabi ke halin tsananin bukatar agaji, bayan tsanantar rikici a ilahirin yankunan kasar 13.

Sai dai bayanan hukumar ta UNHCR na zuwa ne a dai dailokacin da gwamnatin kasar ke bayyana cewa adadin mutane dubu dari 3 ne rikicin kasar y araba da muhallansu sabanin kusan rabin miliyan da hukumar ta bayyana.

Tun daga shekarar 2015 ne Burkina Faso ta fara fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi, wanda kwao yanzu yayi sanadin mutuwar fararen hula 600 ko da dai kungiyoyin agaji sun yi ikirarin cewa adadin ka iya kai fiye da dubu guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.