Isa ga babban shafi
Mali

Firaministan Mali ya jagoranci bikin karbe makamai daga hannun yan tawaye

Dakarun tsaron Mali da Burkina Faso cikin aikin sintiri na ayyukan G5 sahel
Dakarun tsaron Mali da Burkina Faso cikin aikin sintiri na ayyukan G5 sahel Daphné BENOIT / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Firaministan Mali Boubou Cisse a jiya juma’a yayinda yake ziyara garin Mopti ya jagoranci bikin soma mika makamai daga hannun mayaka dubu 8500 a tsakiyar kasar.

Talla

Yunkurin Firaministan kasar na zuwa ne a wani lokaci da kasar ta Mali ke fuskantar hare-hare daga mayankan jihadi.

Wata majiyar tsaro ta tseguntawa kamfanin dilancin labaren Faransa cewa akala mayaka 200 ne yanzu haka suka mika makaman suzuwa hukumomin a garin Mopti.

Shugaban hukumar dake da nauyin tattara wadanan makamai Zahabi Ould Sidy Mohamed yace akala mutane dubu 8.504 ne hukumar ta yi rijistan su ake kuma sa ran za su muka makaman su nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.